1 Suna cikin yin magana da jama'a sai firistoci da shugaban dogaran Haikali da Sadukiyawa suka ji haushi ƙwarai, suka aukar musu,
2 don suna koya wa jama'a, suna tabbatar da tashi daga matattu, suna misali da Yesu.
3 Sai suka kama su, suka sa su a gidan waƙafi kafin gobe, don magariba ta riga ta yi.
4 Amma da yawa daga cikin waɗanda suka ji wa'azin sun ba da gaskiya, har jimillarsu ta kai wajen mutum dubu biyar.
5 Kashegari shugabanninsu da dattawansu da malamansu na Attaura suka taru a Urushalima,