15 Bayan sun umarce su, su fita daga majalisa, suka yi shawara da juna,
16 suka ce, “Yaya za mu yi da mutanen nan? Don hakika sanannen abu ne ga dukan mazauna Urushalima, cewa an yi wata tabbatacciyar mu'ujiza ta wurinsu, ba mu kuwa da halin yin mūsawa.
17 Amma don kada abin ya ƙara bazuwa a cikin mutane, sai mu yi musu kashedi, kada su kuskura su ƙara yi wa kowa magana, suna kama wannan suna.”
18 Sai suka kirawo manzannin, suka kwaɓe su, kada su kuskura su yi wa kowa magana, ko su ƙara koyarwa suna kama sunan Yesu.
19 Amma Bitrus da Yahaya suka mayar musu da jawabi suka ce, “To, in daidai ne a gun Allah mu fi jin taku da ta Allah, sai ku duba ku gani.
20 Domin mu kam, ba yadda za a yi sai mun faɗi abin da muka ji, muka kuma gani.”
21 Da kuma suka daɗa yi musu kashedi, suka sake su, don sun rasa yadda za su hore su saboda jama'a, domin dukan mutane suna ɗaukaka Allah saboda abin da ya auku.