24 Su kuwa da jin haka, sai suka ɗaga muryarsu ga Allah da nufi ɗaya, suka ce, “Ya Mamallaki, Mahaliccin sama, da ƙasa, da teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu,
25 wanda ta Ruhu Mai Tsarki, ta bakin kakanmu Dawuda baranka, ka ce,‘Don me al'ummai suka husata?Kabilai kuma suka yi makidar al'amuran wofi?
26 Sarakunan duniya sun kafa dāga,Mahukunta kuma sun haɗa kai,Suna gāba da Ubangiji, da kuma Almasihunsa.’
27 Gama hakika Hirudus da Buntus Bilatus sun haɗa kai a birnin nan tare da al'ummai da jama'ar Isra'ila gāba da Yesu Baranka mai tsarki, wanda ka maishe shi Almasihu.
28 Sun haɗa kai domin su yi dukan abin da ka ƙaddara zai auku, bisa ga ikonka da nufinka.
29 Yanzu kuma ya Ubangiji, dubi wannan kashedin nasu, ka yi wa bayinka baiwar yin maganarka da iyakar ƙarfin hali,
30 kana kuma miƙo hannunka kana warkarwa, ana kuma yin mu'ujizai da abubuwan al'ajabi albarkacin sunan Baranka mai tsarki Yesu.”