27 Gama hakika Hirudus da Buntus Bilatus sun haɗa kai a birnin nan tare da al'ummai da jama'ar Isra'ila gāba da Yesu Baranka mai tsarki, wanda ka maishe shi Almasihu.
28 Sun haɗa kai domin su yi dukan abin da ka ƙaddara zai auku, bisa ga ikonka da nufinka.
29 Yanzu kuma ya Ubangiji, dubi wannan kashedin nasu, ka yi wa bayinka baiwar yin maganarka da iyakar ƙarfin hali,
30 kana kuma miƙo hannunka kana warkarwa, ana kuma yin mu'ujizai da abubuwan al'ajabi albarkacin sunan Baranka mai tsarki Yesu.”
31 Bayan sun yi addu'a, wurin da suke a tattare ya raurawa. Sai duk aka cika su da Ruhu Mai Tsarki, suka yi ta faɗar maganar Allah gabagaɗi.
32 To, duk taron da suka ba da gaskiya kuwa nufinsu ɗaya ne, ra'ayinsu ɗaya, ba kuma waninsu da ya ce abin da ya mallaka nasa ne, sai dai kome nasu ne baki ɗaya.
33 Manzanni kuma suka yi shaida da tabbatarwa mai ƙarfi a kan tashin Ubangiji Yesu daga matattu. Alheri mai yawa yana tare da kowannensu,