4 Amma da yawa daga cikin waɗanda suka ji wa'azin sun ba da gaskiya, har jimillarsu ta kai wajen mutum dubu biyar.
5 Kashegari shugabanninsu da dattawansu da malamansu na Attaura suka taru a Urushalima,
6 tare da Hanana, babban firist, da Kayafa, da Yahaya, da Iskandari, da kuma duk waɗanda suke dangin babban firist.
7 Da suka tsai da su a tsakiya, suka tuhume su, suka ce, “Da wane iko ne, ko kuwa da wane suna ne, kuka yi haka?”
8 Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya ce musu, “Ya ku shugabannin jama'a, da dattawa,
9 in dai ana tuhumarmu ne yau a kan alherin da aka yi wa gajiyayyen mutumin nan, ta yadda aka warkar da shi,
10 to, sai ku sani, ku duka, da kuma duk jama'ar Isra'ila, da sunan Yesu Almasihu Banazare, wanda ku kuka gicciye, wanda kuma Allah ya tashi shi daga matattu, albarkacinsa ne mutumin nan yake tsaye a gabanku lafiyayye.