6 Waɗannan ne aka gabatar a gaban manzannin. Bayan sun yi addu'a kuma, suka ɗora musu hannu.
7 Maganar Allah kuwa sai ƙara haɓaka take yi, yawan masu bi kuma a birnin Urushalima sai ta ƙaruwa yake yi ƙwarai da gaske, firistoci masu yawan gaske kuma suka yi na'am da bangaskiyar nan.
8 To, Istifanas, cike da alheri da iko, ya yi ta yin manyan al'ajabai da mu'ujizai a cikin jama'a.
9 Sa'an nan waɗansu na majami'ar da ake kira majami'ar Libartinawa, wato Kuraniyawa da Iskandariyawa, da kuma waɗansu daga ƙasar Kilikiya da ta Asiya, suka tasar wa Istifanas da muhawwara.
10 Amma ko kaɗan ba dama su yi masa mūsu, domin ya yi magana da hikima, Ruhu na iza shi.
11 Sai suka zuga mutane a asirce, su kuwa suka ce, “Mun ji shi yana zagin Musa, yana saɓon Allah.”
12 Ta haka suka ta da hankalin jama'a, da shugabanni, da malaman Attaura, su kuma suka aukar masa, suka kama shi, suka kawo shi a gaban majalisa.