14 Sai Yusufu ya aika wa ubansa Yakubu yă zo, da kuma dukan 'yan'uwansa, mutum saba'in da biyar.
15 Sai Yakubu ya tafi Masar. A can ma ya mutu, shi da kakanninmu.
16 Sai aka ɗebo su aka mai da su Shekem, aka sa su a kabarin da Ibrahim ya saya da kuɗi azurfa a wurin 'ya'yan Hamor a nan Shekem.
17 “Amma da lokacin cikar alkawarin da Allah ya yi wa Ibrahim ya gabato, jama'ar suka ƙaru, suka yawaita ƙwarai a ƙasar Masar,
18 har aka yi wani sarki a Masar, wanda bai san ko wane ne Yusufu ba.
19 Wannan sarki kuwa ya cuci kabilarmu, yana gwada wa kakanninmu tasku, yana sawa a yar da jariransu, don kada su rayu.
20 A lokacin nan ne aka haifi Musa, yaro kyakkyawan gaske. Sai aka rene shi wata uku a gidan ubansa.