1 Shawulu kuwa yana goyon bayan kisan Istifanas.A ran nan kuwa wani babban tsanani ya auko wa Ikkilisiyar da take Urushalima. Duk aka warwatsa su a lardin Yahudiya da na Samariya, sai dai manzannin kawai.
2 Sai waɗansu mutane masu bautar Allah suka binne Istifanas, suka yi masa kuka ƙwarai.
3 Amma Shawulu ya yi ta yi wa Ikkilisiya ɓarna ƙwarai da gaske, yana shiga gida gida, yana jan mata da maza, yana jefa su a kurkuku.
4 To, waɗanda aka warwatsar nan kuwa, suka yi ta zazzagawa suna yin bishara.