1 Shawulu kuwa yana kan tsananta kashedi da gāba da masu bin Ubangiji, cewa zai kashe su, sai ya je wurin babban firist,
2 ya roƙe shi ya yi masa wasiƙu zuwa majami'un Dimashƙu, don in ya sami masu bin wannan hanya, mata ko maza, yă zo da su birnin Urushalima a ɗaure.
3 Yana tafiya ke nan, ya yi kusa da Dimashƙu, ba zato sai ga wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi.
4 Sai ya fāɗi, ya kuma ji wata murya tana ce masa, “Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?”
5 Shi kuma ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Sai ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.