12 har ma a cikin wahayi ya ga wani mutum, mai suna Hananiya, ya shigo ya ɗora masa hannu, don ya sāke samun ganin gari.”
13 Amma Hananiya ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, na sha jin labarin mutumin nan gun mutane da yawa, kan yawan muguntar da ya yi wa tsarkakanka a Urushalima.
14 Ga shi kuma manyan firistoci sun ba shi izini ya ɗaure duk mai yin addu'a da sunan har a nan ma.”
15 Amma Ubangiji ya ce masa, “Kai dai, je ka, domin shi ma'aikacina ne zaɓaɓɓe, domin yă sanar da sunana ga al'ummai, da sarakuna, da kuma Isra'ilawa.
16 Domin zan sanar da shi yawan wuyar da lalle zai sha saboda sunana.”
17 Sai Hananiya ya tafi, ya shiga gidan. Da ya ɗora masa hannu, ya ce, “Ya ɗan'uwana Shawulu, Ubangiji ne ya aiko ni, wato Yesu, wanda ya bayyana a gare ka a kan hanyar da ka biyo, domin ka sāke gani, a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.”
18 Nan take sai wani abu kamar ɓawo ya faɗo daga idanunsa, sai ya sāke gani. Sa'an nan ya tashi, aka yi masa baftisma.