31 Sa'an nan ne Ikkilisiyar duk ƙasar Yahudiya, da ta Galili, da ta Samariya ta sami lafiya, ta ingantu sosai, suna tafiyar da al'amuransu da tsoron Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki na taimakonsu, har suka yawaita.
32 To, da Bitrus ya zazzaga lardi duka, sai kuma ya je wurin tsarkakan nan da suke zaune a Lidda.
33 Nan ya tarar da wani mutum, mai suna Iniyasu, wanda yake kwance a kan gado shekara takwas, yana shanyayye.
34 Sai Bitrus ya ce masa, “Iniyasu, Yesu Almasihu ya warkar da kai. Tashi ka kintsa gadonka.” A nan tāke ya tashi.
35 Duk mutanen Lidda da na ƙasar Sarona kuwa suka gan shi, suka juyo ga Ubangiji.
36 A Yafa kuwa akwai wata mai bi, mai suna Tabita, wato Dokas ke nan. Matar nan kuwa lazimar aiki nagari ce, da kuma gudunmawa.
37 A lokacin nan ta yi rashin lafiya, ta mutu. Da suka yi mata wanka, suka shimfiɗe ta a kan bene.