5 Shi kuma ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Sai ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.
6 Amma ka tashi ka shiga gari, can za a faɗa maka abin da za ka yi.”
7 Abokan tafiyarsa kuwa suka rasa bakin magana, suna jin muryar, amma ba su ga kowa ba.
8 Sai Shawulu ya tashi, amma da ya buɗe ido ya kasa gani. Sai aka yi masa jagora, aka kai shi Dimashƙu.
9 Kwanansa uku ba ya gani, ba ya kuma ci, ba ya sha.
10 To, akwai wani mai bi a Dimashƙu, mai suna Hananiya. Ubangiji ya yi masa magana cikin wahayi ya ce, “Hananiya.” Shi kuwa ya ce, “Na'am, ya Ubangiji.”
11 Sai Ubangiji ya ce masa, “Tashi ka tafi titin nan da ake kira Miƙaƙƙiye, ka tambaya a gidan Yahuza, ko akwai wani mutumin Tarsus, mai suna Shawulu, ga shi nan, yana addu'a,