1 Bayan shekara goma sha huɗu na sāke komawa Urushalima tare da Barnaba, na kuma ɗauki Titus.
2 Da umarnin wahayi ne na tafi, har na rattaba musu bisharar da nake yi a cikin al'ummai, amma a keɓance a gaban waɗansu shugabannin ikkilisiya, kada himmar da nake yi, ko wadda na riga na yi, ta zamana ta banza ce.
3 Kai, ko Titus ma da yake a tare da ni, ba a tilasta masa yin kaciya ba, ko da yake shi Bahelene ne.
4 Maganar nan ta tashi saboda 'yan'uwan ƙaryar nan ne, da aka shigo da su a asirce, waɗanda suka saɗaɗo su yi ganganen 'yancinmu da muke da shi ta wurin Almasihu Yesu, don dai su sa mu bauta.
5 Amma ko kaɗan ba mu sakar musu ba, ko da taƙi, domin gaskiyar bishara tă zaune muku.
6 Waɗanda kuma aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne (ko su wane ne, ai, duk ɗaya ne a guna, domin Allah ba ya tāra), ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙare ni da kome ba.
7 Amma da suka ga an amince mini in yi wa marasa kaciya bishara, kamar yadda aka amince wa Bitrus ya yi wa masu kaciya bishara,