1 Ya ku 'yan'uwa, in an kama mutum yana a cikin yin laifi, ku da kuke na ruhu, sai ku komo da shi a kan hanya da tawali'u, kowa yana kula da kansa kada shi ma ya burmu.
2 Ku ɗauki wahalar juna, ta haka za ku cika shari'ar Almasihu.
3 Kowa ya zaci shi wani abu ne, alhali kuwa shi ba kome ba ne, ya ruɗi kansa ke nan.
4 Kowa yă auna aikinsa ya gani, sa'an nan ne zai iya gadara da maƙaminsa shi da kansa, ba sai ya gwada kansa da wani ba.
5 Lalle kowa yă ji da kayansa.
6 Duk wanda aka koya wa Maganar, yă ci moriyar abubuwansa na alheri tare da mai koyarwa.
7 Kada fa a yaudare ku, ai, ba a iya zambatar Allah. Duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba.