1 Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, tare da Timoti, ɗan'uwanmu,
2 zuwa ga tsarkaka da amintattun 'yan'uwa cikin Almasihu da suke a Kolosi.Alheri da salamar Allah Ubanmu su tabbata a gare ku.
3 A kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu, duk sa'ad da muke yi muku addu'a,
4 saboda mun ji labarin bangaskiyarku ga Almasihu Yesu, da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan tsarkaka,
5 saboda bege ga abin da aka tanadar muku a sama. Kun riga kun ji labarin wannan a maganar gaskiya,
6 wato, bisharar da ta zo muku, kamar yadda ta zo wa duniya duka, tana hayayyafa, tana kuma ƙara yaɗuwa, kamar yadda take yi a tsakaninku tun daga ranar da kuka ji, kuka kuma fahimci alherin Allah na hakika.