3 A kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu, duk sa'ad da muke yi muku addu'a,
4 saboda mun ji labarin bangaskiyarku ga Almasihu Yesu, da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan tsarkaka,
5 saboda bege ga abin da aka tanadar muku a sama. Kun riga kun ji labarin wannan a maganar gaskiya,
6 wato, bisharar da ta zo muku, kamar yadda ta zo wa duniya duka, tana hayayyafa, tana kuma ƙara yaɗuwa, kamar yadda take yi a tsakaninku tun daga ranar da kuka ji, kuka kuma fahimci alherin Allah na hakika.
7 Haka ma kuka koya wurin Abafaras, ƙaunataccen abokin bautarmu. Shi amintaccen mai hidima ne na Almasihu a madadinmu,
8 ya kuma sanasshe mu ƙaunar da kuke yi cikin Ruhu.
9 Shi ya sa tun a ran da muka ji labarin, ba mu fāsa yi muku addu'a ba, muna roƙo a cika ku da sanin nufin Allah da matuƙar hikima da fahimta na ruhu,