9 Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun yar da halinku na dā, da ayyukansa,
10 kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa.
11 A nan kam, ba hanyar nuna bambanci a tsakanin Ba'al'umme da Bayahude, ko mai kaciya da marar kaciya, ko bare da baubawa, ko ɗa da bawa, sai dai Almasihu shi ne kome, shi kuma yake cikinmu duka.
12 Saboda haka, sai ku ɗauki halin tausayi, da kirki, da tawali'u, da salihanci, da haƙuri, idan ku zaɓaɓɓu ne na Allah, tsarkaka, ƙaunatattu,
13 kuna jure wa juna, in kuma wani yana da ƙara game da wani, sai su yafe wa juna. Kamar yadda Ubangiji ya yafe muku, ku kuma sai ku yafe.
14 Fiye da waɗannan duka, ku ɗau halin ƙauna, wadda dukkan kammala take ƙulluwa a cikinta.
15 Salamar Almasihu kuma tă mallaki zuciyarku, domin lalle ga haka aka kira ku in kuna jiki guda, ku kuma kasance masu gode wa Allah.