1 Ku iyayengiji kuma, ku riƙi bayinku da gaskiya da daidaita, da yake kun sani ku ma kuna da Ubangiji a Sama.
2 Ku lazamci yin addu'a, kuna zaune a faɗake a kanta sosai, tare da gode wa Allah,
3 mu ma ku yi mana addu'a Allah ya buɗe mana hanyar yin Maganarsa, mu sanar da asirin Almasihu, wanda saboda shi ne nake a ɗaure,
4 domin in bayyana shi sosai, kamar yadda ya kamata in faɗa.
5 Ku tafiyar da al'amuranku da hikima a cikin zamanku tare da marasa bi, kuna matuƙar amfani da lokaci.
6 A kullum maganarku ta zama mai ƙayatarwa, mai daɗin ji, domin ku san irin amsar da ta dace ku ba kowa.