51 Manyan ayyuka da ya yi,Masu girmankai, su da dabarbarunsu ya warwatsa.
52 Ya firfitar da sarakuna a sarauta,Ya ɗaukaka ƙasƙantattu.
53 Mayunwata ya ƙosar da abubuwan alheri,Mawadata kuwa ya sallame su hannu wofi.
54 Ya taimaka wa baransa Isra'ila,Domin yana tunawa da jinƙansa.
55 Ya cika faɗarsa ga kakanninmu,Ga Ibrahim da zuriyarsa, har abada.”
56 Maryamu kuma ta zauna tare da Alisabatu wajen wata uku, sa'an nan ta koma gida.
57 To, lokacin Alisabatu na haihuwa ya yi, ta kuwa haifi ɗa namiji.