57 To, lokacin Alisabatu na haihuwa ya yi, ta kuwa haifi ɗa namiji.
58 Sai maƙwabta da 'yan'uwanta suka ji yadda Ubangiji ya ji ƙanta ƙwarai, har suka taya ta farin ciki.
59 Sai ya zamana a rana ta takwas suka zo yi wa ɗan yaron kaciya. A dā za su sa masa sunan ubansa, Zakariya,
60 amma uwa tasa ta ce, “A'a, Yahaya za a sa masa.”
61 Sai suka ce mata, “Ai kuwa, ba wani ɗan'uwanku mai suna haka.”
62 Sai suka alamta wa ubansa, suna neman sunan da yake so a sa masa.
63 Sai ya nema a ba shi allo, sa'an nan ya rubuta, “Sunansa Yahaya.” Duka suka yi mamaki.