1 Wata rana Yesu yana addu'a a wani wuri. Bayan da ya gama, sai wani a cikin almajiransa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka koya mana addu'a, kamar yadda Yahaya ya koya wa almajiransa.”
2 Sai ya ce musu, “In kuna addu'a ku ce,‘Ya Uba, a kiyaye sunanka da tsarki,Mulkinka yă zo,
3 Ka ba mu abincin yau da na kullum.
4 Ka gafarta mana zunubanmu, gama mu ma muna gafarta wa duk wanda yake yi mana laifi.Kada ka kai mu wurin jaraba.’ ”
5 Ya kuma gaya musu, “Misali, idan waninku yana da amini, ya je wurinsa da tsakar dare ya ce masa, ‘Wāne, ranta mini gurasa uku mana,