36 In kuwa duk jikinka ya cika da haske, ba inda ke da duhu, ai, duk sai ya haskaka gaba ɗaya, kamar yadda hasken fitila take haskaka maka.”
37 Yesu yana magana, sai wani Bafarisiye ya kira shi cin abinci. Ya shiga cin abincin.
38 Sai Bafarisiyen ya yi mamakin ganin yadda Yesu zai ci abinci ba da fara wanke hannu ba.
39 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ku Farisiyawa kam, kukan wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki cike kuke da zalunci da mugunta.
40 Ku marasa azanci! Ashe, wanda ya yi bayan, ba shi ya yi cikin ba?
41 Gara ku tsarkake cikin, sa'an nan kome zai tsarkaka a gare ku.
42 “Kaitonku, Farisiyawa! Ga shi, kuna fitar da zakkar na'ana'a da karkashi, da kuma kowane ganyen miya. Amma kun ƙi kula da aikata gaskiya da ƙaunar Allah. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da waɗancan ba.