49 “Wuta ce na zo in zuba wa duniya. Sona fa? A ce ta huru!
50 Ina da baftismar da za a yi mini, na kuwa ɗokanta ƙwarai har a yi mini ita!
51 Kuna tsammani na zo ne in kawo salama a duniya? A'a, ina gaya muku, sai dai rabuwa.
52 Nan gaba, a gida guda mutum biyar za su kasu biyu, uku na gāba da biyu, biyu kuma na gāba da uku.
53 Ta haka, za su rabu. Uba yana gāba da ɗansa, ɗan kuma yana gāba da ubansa, uwa tana gāba da 'ya tata, 'yar kuma tana gāba da uwa tata, suruka tana gāba da matar ɗanta, matar ɗan kuma tana gāba da suruka tata.”
54 Ya kuma ce wa taron, “In kun ga girgije yana tasowa daga yamma, nan da nan kukan ce, ‘Za a yi ruwa.’ Sai kuwa a yi.
55 In kuwa kun ga iskar kudu tana busowa, kukan ce, ‘Za a yi matsanancin zafi.’ Sai kuwa a yi.