1 Ya kuma ba su wani misali cewa ya kamata kullum su yi addu'a, kada kuma su karai.
2 Ya ce, “A wani gari an yi wani alƙali marar tsoron Allah, marar kula da mutane.
3 A garin nan kuwa da wata wadda mijinta ya mutu, sai ta riƙa zuwa wurinsa, tana ce masa, ‘Ka shiga tsakanina da abokin gābana.’
4 Da fari ya ƙi, amma daga baya sai ya ce a ransa, ‘Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane,
5 amma saboda gwauruwar nan ta dame ni, sai in bi mata hakkinta, don kada ta gajishe ni da yawan zuwa.’ ”