3 A garin nan kuwa da wata wadda mijinta ya mutu, sai ta riƙa zuwa wurinsa, tana ce masa, ‘Ka shiga tsakanina da abokin gābana.’
4 Da fari ya ƙi, amma daga baya sai ya ce a ransa, ‘Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane,
5 amma saboda gwauruwar nan ta dame ni, sai in bi mata hakkinta, don kada ta gajishe ni da yawan zuwa.’ ”
6 Sai Ubangiji ya ce, “Ku ji fa abin da alƙalin nan marar gaskiya ya faɗa!
7 Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke yi masa kuka dare da rana hakkinsu ba? Zai yi jinkiri a wajen taimakonsu ne?
8 Ina gaya muku, zai biya musu hakkinsu, da wuri kuwa. Amma kuwa sa'ad da Ɗan Mutum ya zo, zai tarar da bangaskiya a duniya ne?”
9 Sai kuma ya ba da misalin nan ga waɗansu masu amince wa kansu, wai su masu adalci ne, har suna raina sauran mutane, ya ce,