12 Ga alamar da za ku gani, za ku sami jariri rufe da zanen goyo, kwance a komin dabbobi.”
13 Ba labari sai ga taron rundunar Sama tare da mala'ikan nan, suna yabon Allah, suna cewa,
14 “Ɗaukaka ga Allah ta tabbata, can cikin Sama mafi ɗaukaka.A duniya salama ta tabbata, ga mutanen da yake murna da su matuƙa.”
15 Da mala'iku suka tafi daga gare su suka koma Sama, sai makiyayan suka ce wa juna, “Mu tafi Baitalami yanzu, mu ga abin nan da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar da mu.”
16 Sai suka tafi da hanzari, suka sami Maryamu da Yusufu, da kuma jaririn kwance a komin dabbobi.
17 Da suka gan shi, suka bayyana maganar da aka faɗa musu game da wannan ɗan yaro.
18 Duk waɗanda suka ji kuma, suka yi ta al'ajabin abin da makiyayan nan suka faɗa musu.