18 Duk waɗanda suka ji kuma, suka yi ta al'ajabin abin da makiyayan nan suka faɗa musu.
19 Maryamu kuwa sai ta riƙe duk abubuwan da aka faɗa, tana biya su a zuci.
20 Makiyayan suka koma, suna ta ɗaukaka Allah, suna yabonsa, saboda duk abin da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.
21 Da rana ta takwas ta kewayo da za a yi masa kaciya, aka sa masa suna Yesu, wato sunan da mala'ika ya faɗa kafin ya zauna a ciki.
22 Da kwanakin tsarkakewarsu suka cika bisa ga Shari'ar Musa, suka kawo shi Urushalima, su miƙa shi ga Ubangiji
23 (kamar dai yadda yake a rubuce a Shari'ar Ubangiji cewa, “Duk ɗan farin da aka haifa, za a ce da shi tsattsarka ne Ubangiji”),
24 su kuma yi hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Shari'ar Ubangiji cewa, “Kurciyoyi biyu, ko kuwa 'yan shila biyu.”