25 To, akwai wani mutum a Urushalima, mai suna Saminu, adali, mai bautar Allah, yana kuma ɗokin ganin ta'aziyyar Isra'ila. Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi.
26 Ruhu Mai Tsarki kuwa ya riga ya bayyana masa, cewa ba zai mutu ba sai ya ga Almasihun Ubangiji.
27 Ruhu na iza shi, sai ya shiga Haikalin. Da iyayen suka shigo da ɗan yaron nan Yesu, su yi masa yadda ka'idar Shari'ar ta ce,
28 sai Saminu ya rungume shi, ya yi wa Allah godiya, ya ce,
29 “Yanzu kam, ya Mamallaki,Sai ka sallami bawanka lafiya,Bisa ga abin da ka faɗa,
30 Don na ga cetonka zahiri,
31 Da ka shirya a gaban kabilai duka,