42 Da ya shekara goma sha biyu, sai suka tafi tare da shi bisa ga al'adarsu a lokacin Idi.
43 Da aka gama idin kuma, suna cikin komowa, sai yaron, wato Yesu, ya tsaya a Urushalima, ba da sanin iyayensa ba.
44 Su kuwa suka yi ta tafiya yini guda, suna zaton yana cikin ayari. Sai suka yi ta cigiyarsa cikin 'yan'uwansu da idon sani.
45 Da ba su same shi ba, suka koma Urushalima, suna ta cigiyarsa.
46 Sai kuma a rana uku suka same shi a Haikalin zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu, yana kuma yi musu tambayoyi.
47 Duk waɗanda suka ji shi kuwa suka yi al'ajabin irin fahimtarsa da amsoshinsa.
48 Da suka gan shi suka yi mamaki, sai uwa tasa ta ce masa, “Ya kai ɗana, yaya ka yi mana haka? Ga shi nan, ni da babanka muna ta nemanka duk ranmu a ɓace.”