1 Wata rana yana koyar da mutane a Haikali, yana yi musu bishara, sai ga manyan firistoci da malaman Attaura, da shugabanni suka matso,
2 suka ce masa, “Gaya mana da wane izini kake yin abubuwan nan, ko kuwa wa ya ba ka izinin?”
3 Sai ya amsa musu ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku gaya mini,
4 baftismar da Yahaya ya yi, daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?”
5 Sai suka yi muhawwara da juna suka ce, “In mun ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’
6 In kuwa muka ce, ‘Ta mutum ce,’ sai duk jama'a su jajjefe mu, don sun tabbata Yahaya annabi ne.”