28 suka tambaye shi suka ce, “Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan ɗan'uwan mutum ya mutu, ya bar matarsa ba ɗa, lalle mutumin ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya.
29 To, an yi waɗansu 'yan'uwa maza guda bakwai. Na farko ya yi aure, ya mutu bai bar na baya ba.
30 Na biyun,
31 da na ukun kuma suka aure ta. Haka dai, duk bakwai ɗin suka aure ta, suka mutu, ba wanda ya bar ɗa.
32 Daga baya kuma ita matar ta mutu.
33 To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai ɗin sun aure ta.”
34 Sai Yesu ya ce musu, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna aurarwa.