40 Daga nan kuma ba su yi ƙarfin halin tambayarsa wani abu ba.
41 Amma ya ce musu, “Ƙaƙa za su ce Almasihu ɗan Dawuda ne?
42 Domin Dawuda da kansa a Zabura ya ce,‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,“Zauna a damana,
43 Sai na sa ka take maƙiyanka.” ’
44 Dawuda ya ce shi Ubangiji ne. To, ƙaƙa zai zama ɗansa?”
45 Ya ce wa almajiransa a gaban dukan jama'a,
46 “Ku yi hankali da malaman Attaura, masu son yawo a cikin manyan riguna, masu so a gaishe su a kasuwa, masu son mafifitan mazaunai a majami'u, da mazaunan alfarma a wurin biki.