16 Ko da iyayenku ma da 'yan'uwanku, da danginku, da abokanku, sai sun bāshe ku, su kuma sa a kashe waɗansunku.
17 Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana.
18 Amma ba gashin kanku ko ɗaya da zai yi ciwo.
19 Jurewarku ce za ta fisshe ku.”
20 “Sa'ad da kuka ga rundunonin yaƙi sun kewaye Urushalima, sa'an nan ku tabbata ana kusan ribɗe ta.
21 Sa'an nan waɗanda suke a ƙasar Yahudiya, su gudu su shiga duwatsu, na birni su fice, na ƙauye kuma kada su shiga birni.
22 Saboda lokacin sakamako ne, don a cika duk abin da yake rubuce.