52 Shi ne ya tafi wurin Bilatus, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.
53 Sai ya sauko da shi, ya sa shi a likkafanin lilin, ya sa shi a wani kabari da aka fafe dutse aka yi, wanda ba a taɓa sa kowa ba.
54 Ran nan kuwa ranar shiri ce, Asabar kuma ta doso.
55 Matan nan kuwa da suka zo tare da shi daga ƙasar Galili, suka bi baya, suka duba kabarin da yadda kuma aka sa jikinsa.
56 Sai suka koma, suka shirya kayan ƙanshi da man shafawa.Ran Asabar kuwa, sai suka huta bisa ga umarni.