13 A ran nan kuma sai ga waɗansu biyu suna tafiya wani ƙauye, mai suna Imuwasu, nisansa daga Urushalima kuwa kusan mil bakwai ne.
14 Suna ta zance da juna a kan dukan al'amuran da suka faru.
15 Ya zamana tun suna magana, suna tunani tare, sai Yesu da kansa ya matso, suka tafi tare.
16 Amma idanunsu a rufe, har ba su gane shi ba.
17 Yesu ya ce musu, “Wace magana ce kuke yi da juna a tafe?” Sai suka tsaya cik, suna baƙin ciki.
18 Sai ɗayansu, mai suna Kiliyobas, ya amsa masa ya ce, “Ashe, kai kaɗai ne baƙo a Urushalima, da ba ka san abubuwan da suka faru a can, 'yan kwanakin nan ba?”
19 Sai ya ce musu, “Waɗanne abubuwa?” Suka ce masa, “Game da Yesu Banazare ne, wanda yake annabi mai manyan ayyuka da ƙwaƙƙwarar magana a gaban Allah da dukan mutane,