2 a zamanin da Hanana da Kayafa suke manyan firistoci, Maganar Allah ta zaike wa Yahaya ɗan Zakariya a jeji.
3 Sai ya zaga duk lardin bakin Kogin Urdun, yana wa'azi, cewa mutane su tuba a yi musu baftisma, domin a gafarta musu zunubansu,
4 yadda yake a rubuce a Littafin Annabi Ishaya cewa,“Muryar mai kira a jeji tana cewa,Ku shirya wa Ubangiji tafarki,Ku miƙe hanyoyinsa,
5 Za a cike kowane kwari,Kowane dutse da kowane tsauni za a baje su.Za a miƙe karkatattun wurare,Za a bi da hanyoyin da ba su biyu ba.
6 Dukkan 'yan adam kuma za su ga ceton Allah.”
7 Saboda haka, Yahaya ya ce wa taron jama'ar da yake zuwa domin ya yi musu baftisma, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa?
8 Ku yi aikin da zai nuna tubanku, kada ma ku ko fara cewa a ranku Ibrahim ne ubanku. Ina dai gaya muku Allah yana da iko ya halitta wa Ibrahim 'ya'ya daga duwatsun nan.