7 Waɗansu kuma suka fāɗi cikin ƙaya, suka tashi tare, har ƙayar ta sarƙe su.
8 Waɗansu kuwa suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka girma, suka yi ƙwaya riɓi ɗari ɗari.” Da ya faɗi haka, sai ya ta da murya ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”
9 Almajiransa suka tambaye shi ma'anar misalin.
10 Sai ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Allah. Amma ga sauran sai da misali, don gani kam, su gani, amma ba za su gane ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba.
11 “To, misalin shi ne, irin Maganar Allah ne.
12 Waɗanda suka fāɗi a hanya su ne kwatancin waɗanda suka ji Maganar Allah, sa'an nan Iblis ya zo ya ɗauke Maganar daga zuciyarsu, don kada su ba da gaskiya su sami ceto.
13 Na kan dutsen kuwa su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar, sai su karɓa da farin ciki. Su kam, ba su da tushe. Sukan ba da gaskiya 'yan kwanaki kaɗan, amma a lokacin gwaji, sai su bauɗe.