14 To, bayan an tsare Yahaya, sai Yesu ya shigo ƙasar Galili, yana yin bisharar Allah,
15 yana cewa, “Lokaci ya yi, Mulkin Allah ya kusato. Ku tuba, ku gaskata da bishara.”
16 Yana wucewa ta bakin Tekun Galili, sai ya ga Bitrus da Andarawas ɗan'uwansa, suna jefa taru a teku, don su masunta ne.
17 Yesu ya ce musu, “Ku bi ni, zan mai da ku masuntan mutane.”
18 Nan da nan kuwa suka watsar da tarunansu, suka bi shi.
19 Da ya ci gaba kaɗan, sai ya ga Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya, suna cikin jirginsu suna gyaran taruna.
20 Nan da nan da ya kira su, suka bar ubansu Zabadi a cikin jirgin tare da ma'aikata, suka bi shi.