36 Sai Bitrus da waɗanda suke tare da shi suka bi shi.
37 Da suka same shi, suka ce masa, “Duk ana nemanka.”
38 Ya ce musu, “Mu tafi garuruwan da suke gaba, in yi wa'azi a can kuma, domin saboda haka ne na fito.”
39 Ya gama ƙasar Galili duk yana wa'azi a majami'unsu, yana kuma fitar wa mutane aljannu.
40 Wani kuturu ya zo wurinsa, yana roƙonsa, yana durƙusawa a gabansa, yana cewa, “In ka yarda kana da iko ka tsarkake ni.”
41 Da tausayi ya kama Yesu, sai ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce masa, “Na yarda, ka tsarkaka.”
42 Nan take sai kuturtar ta rabu da shi, ya tsarkaka.