24 Don haka ina dai gaya muku, kome kuka roƙa da addu'a, ku gaskata cewa samamme ne, za ku kuwa samu.
25 Koyaushe kuka tsaya yin addu'a, in akwai wanda kuke jin haushinsa, ku yafe masa, domin Ubanku da yake Sama shi ma yă yafe muku laifofinku. [
26 Amma in ba kwa yafewa, haka Ubanku da yake Sama ma ba zai yafe muku laifofinku ba.]”
27 Suka koma Urushalima. Yana zaga cikin Haikalin sai manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabannin jama'a suka zo wurinsa,
28 suka ce masa, “Da wane izni kake yin waɗannan abubuwa, ko kuwa wa ya ba ka iznin yin haka?”
29 Sai Yesu ya ce musu, “Zan yi muku wata tambaya. Ku ba ni amsa, ni kuwa in gaya muku ko da wane izni nake yin abubuwan nan.
30 To, baftismar da Yahaya ya yi, daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce? Ku ba ni amsa.”