34 Da Yesu ya ga ya yi masa magana da fasaha, sai ya ce masa, “Ba ka nesa da Mulkin Allah.” Bayan wannan kuma ba wanda ya yi ƙarfin halin sāke tambayarsa wani abu.
35 Sa'ad da Yesu yake koyarwa a Haikalin sai ya ce, “Ƙaƙa malaman Attaura za su ce Almasihu ɗan Dawuda ne?
36 Domin Dawuda kansa, ta ikon Ruhu Mai Tsarki ya ce,‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,Zauna a damana,Sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.’
37 Dawuda da kansa ya kira shi Ubangiji. To, ƙaƙa zai zama ɗansa?” Babban taron mutane kuwa sun saurare shi da murna.
38 A koyarwa tasa har ya ce, “Ku yi hankali da malaman Attaura, masu son yawo da manyan riguna, suna so a gaishe su a kasuwa,
39 da kuma mafifitan mazaunai a majami'u, da mazaunan alfarma a wurin biki.
40 Su ne masu cin kayan matan da mazansu suka mutu, da yin doguwar addu'a don ɓad da sawu. Su za a yi wa hukunci mafi tsanani.”