36 Domin Dawuda kansa, ta ikon Ruhu Mai Tsarki ya ce,‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,Zauna a damana,Sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.’
37 Dawuda da kansa ya kira shi Ubangiji. To, ƙaƙa zai zama ɗansa?” Babban taron mutane kuwa sun saurare shi da murna.
38 A koyarwa tasa har ya ce, “Ku yi hankali da malaman Attaura, masu son yawo da manyan riguna, suna so a gaishe su a kasuwa,
39 da kuma mafifitan mazaunai a majami'u, da mazaunan alfarma a wurin biki.
40 Su ne masu cin kayan matan da mazansu suka mutu, da yin doguwar addu'a don ɓad da sawu. Su za a yi wa hukunci mafi tsanani.”
41 Sai ya zauna gaban baitulmalin Haikalin, yana duban yadda jama'a suke zuba kuɗi a ciki. Waɗansu masu arziki da yawa suna zuba kuɗi masu tsoka.
42 Sai ga wata gajiyayyiya da mijinta ya mutu ta zo, ta zuba rabin kobo biyu a ciki, wato kobo ke nan.