4 Sai ya sāke aika musu wani bawa. Shi kuma suka yi masa rotsi, suka wulakanta shi.
5 Ya sāke aiken wani, shi kam, sai suka kashe shi. Haka fa aka yi ta yi da waɗansu da yawa, ana dūkan waɗansu, ana kashe waɗansu.
6 Har yanzu dai yana da sauran ɗaya tak, shi ne makaɗaicin ɗansa. Daga ƙarshe ya aike shi wurinsu, yana cewa, ‘Sā ga girman ɗana.’
7 Amma manoman nan suka ce wa juna, ‘Ai, wannan shi ne magajin. Ku zo mu kashe shi, gādon yă zama namu.’
8 Sai suka kama shi, suka kashe shi, suka jefar da shi bayan shinge.
9 To, me ubangijin garkan nan zai yi? Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba waɗansu garkar.
10 Ashe, ba ku taɓa karanta wannan Nassi ba? cewa,‘Dutsen da magina suka ƙi,Shi ne ya zama mafificin dutsen gini.