1 Yesu na fita daga Haikalin, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Malam, dubi irin duwatsun nan da gine-ginen nan!”
2 Sai Yesu ya ce masa, “Ka ga manyan gine-ginen nan? Ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗan'uwansa, da ba za a baje shi ba.”
3 Yana zaune a kan Dutsen Zaitun wanda yake kallon Haikalin sai Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, da Andarawas suka tambaye shi a keɓe suka ce.
4 “Gaya mana yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Wace alama kuma za a gani sa'ad da suke shirin aukuwa?”
5 Sai Yesu ya fara ce musu, “Ku kula fa kada kowa ya ɓad da ku.
6 Mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa su ne ni, har su ɓad da mutane da yawa.