13 Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe zai cetu.”
14 “Sa'ad da kuka ga an kafa mummunan aikin saɓo mai banƙyama a wurin da bai kamata ba (mai karatu fa yă fahimta), to, sai waɗanda suke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu.
15 Wanda yake kan soro kuma kada yă sauko yă shiga gida garin ɗaukar wani abu.
16 Wanda yake gona kuma kada ya koma garin ɗaukar mayafinsa.
17 Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci!
18 Ku yi addu'a kada abin nan ya auku da damuna.
19 A lokacin nan za a yi wata matsananciyar wahala, irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon halittar da Allah ya yi, har ya zuwa yanzu, ba kuwa za a ƙara yi ba har abada.