10 Don ya gane, saboda hassada ne manyan firistoci suka bashe shi.
11 Amma manyan firistocin suka zuga jama'a, gwamma ya sakar musu Barabbas.
12 Sai Bilatus ya sāke ce musu, “To, ƙaƙa zan yi da wanda kuke kira Sarkin Yahudawa?”
13 Sai suka sāke yin ihu suka ce, “A gicciye shi!”
14 Bilatus ya ce musu, “Ta wane hali? Wane mugun abu ne ya yi?” Amma su, sai ƙara ɗaga murya suke yi, suna cewa, “A gicciye shi!”
15 Bilatus kuwa da yake yana son ƙayatar da jama'a, ya sakar musu Barabbas. Bayan ya yi wa Yesu bulala, ya ba da shi a gicciye shi.
16 Sai soja suka tafi da shi cikin fada, wato fadar mai mulkin, suka tara dukkan rundunar soja.