30 Wannan kuwa don sun ce, “Yana da baƙin aljan ne.”
31 Sa'an nan uwa tasa da 'yan'uwansa suka zo. Suna tsaye a waje, sai suka aika masa yă je.
32 Taro kuwa na zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, “Ga tsohuwarka da 'yan'uwanka suna nemanka a waje.”
33 Ya amsa musu ya ce, “Su wane ne tsohuwata da 'yan'uwana?”
34 Sai ya waiwayi waɗanda suke zaune kewaye da shi, ya ce, “Ga tsohuwata a nan da 'yan'uwana!
35 Ai, kowa ya yi abin da Allah yake so, shi ne ɗan'uwana, ita ce 'yar'uwata, ita ce kuma tsohuwata.”