22 Sai ga wani daga cikin shugabannin majami'a, mai suna Yayirus. Da ganin Yesu kuwa ya fāɗi a gabansa,
23 ya roƙe shi da gaske, yana cewa, “'Yata ƙaramar tana bakin mutuwa. Idan dai a ce ka zo ka ɗora mata hannu, sai ta warke ta rayu.”
24 Sai suka tafi tare. Babban taro kuwa na biye da shi, suna matsa tasa.
25 Sai ga wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini,
26 ta kuma sha wahala da gaske a hannun masu magani da yawa, har ta ɓad da duk abin da take da shi, amma duk a banza, sai ma gaba-gaba cutar take yi.
27 Da ta ji labarin Yesu, ta raɓo ta bayansa cikin taron, ta taɓa mayafinsa.
28 Don tā ce a ranta, “Ko da tufarsa ma na taɓa, sai in warke.”