3 Shin, wannan ba shi ne masassaƙin nan ba, ɗan Maryamu, ɗan'uwan su Yakubu, da Yusufu, da Yahuza, da kuma Saminu? 'Yan'uwansa mata kuma ba ga su tare da mu ba?” Suka yi tuntuɓe sabili da shi.
4 Sai Yesu ya ce musu, “Ai, annabi ba ya rasa girma sai dai a garinsu, da cikin 'yan'uwansa, da kuma gidansu.”
5 Bai ko iya yin wata mu'ujiza a can ba, sai dai ya ɗora wa marasa lafiya kaɗan hannu ya warkar da su.
6 Ya yi mamakin rashin bangaskiyarsu.Sai ya zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.
7 Sai ya kira goma sha biyun nan, ya fara aikensu biyu-biyu, ya kuma ba su iko a kan baƙaƙen aljannu.
8 Ya umarce su kada su ɗauki guzuri don tafiyar, ko gurasa, ko burgami, ko kuɗi ma a ɗamararsu, sai dai sanda kawai,
9 amma su sa takalmi, kada kuma su haɗa taguwa biyu.