4 Sai Yesu ya ce musu, “Ai, annabi ba ya rasa girma sai dai a garinsu, da cikin 'yan'uwansa, da kuma gidansu.”
5 Bai ko iya yin wata mu'ujiza a can ba, sai dai ya ɗora wa marasa lafiya kaɗan hannu ya warkar da su.
6 Ya yi mamakin rashin bangaskiyarsu.Sai ya zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.
7 Sai ya kira goma sha biyun nan, ya fara aikensu biyu-biyu, ya kuma ba su iko a kan baƙaƙen aljannu.
8 Ya umarce su kada su ɗauki guzuri don tafiyar, ko gurasa, ko burgami, ko kuɗi ma a ɗamararsu, sai dai sanda kawai,
9 amma su sa takalmi, kada kuma su haɗa taguwa biyu.
10 Ya ce musu, “Duk gidan da kuka sauka, ku zauna a nan har ku tashi.